Daga Fatima Hassan Gagara
Jami’ar Bayero ta Kano ta kara samun daukaka a duniya sakamakon shigar wasu malamanta 3 jerin manyan masana a duniya na Shekarar 2025.
Farfesa Abdurrazzaq G. Habib da Dakta Sanusi Marwana da kuma Dakta Isah Baba Abdullahi sun shiga cikin kashi 2 na manyan masana da suka fi tasiri a duniya na wannan shekara ne a bisa jerin sunayen da Jami’ar Stanford tare da kamfanin Elsevier suka fitar.

Hukumar jami’ar Bayero kuma ta wallafa a jaridarta a karshen mako, tana mai taya su murnar wannan babbar nasarar a duniya.
Farfesa Abdurrazzaq G. Habib ya zo na 22 a duniya a fannin Magungunan Cututtuka na kasashe masu yanayin zafi, saboda bincikensa mai zurfi kan cututtuka masu yaduwa da a yanayin zafi, ayyukansa kuma sun taimaka wajen inganta kula da lafiya da yaki da cututtuka a fadin duniya.
Dakta Saniu Maanan Ma’ajiadan ya zo na 4,113 a duniya a fannin Injiniyan Kayan Aiki. Yana da h-index 14 da i10-index 4, tare da shahararren bincike kan sabbin kayan aiki da kimiyyar fasahar sarrafa su.
Yayin da Dakta Isah Baba Abdullahi ya zo na 4,124 a duniya a fannin Lissafi a ilimin kimiyyar Physics, inda yake da h-index 8 da i10-index 4. Yana da suna wajen hada ilimin lissafi da kimiyyar Physics.
Shugaban Jami’ar Farfesa Haruna Musa ya bayyana wannan cigaba a matsayin babbar nasara ga jami’ar kuma hujja ce da ke nuna irin ci gaban da jami’ar ke samu a fannin bincike a duniya.
“Wannan nasara ta Najeriya ce baki ɗaya. Tana kuma nuna cewa bincikenmu na kai kololuwa a matakin duniya,” in ji shi.
Tsarin fidda gwanaye a ilimin kimiyya na Jerin Stanford–Elsevier na daga cikin ma’aunin da ake girmamawa wajen tantance masana a duniya.
Ana amfani da bayanan Scopus wajen tantance yawan ambaton sunaye, da hadin gwiwa na wallafe-wallafe da kuma yawan wallafe-wallafen da masanin ya yi kafin yaka ga wannan matsayi.
Ana daukar masana da suka fi samun ambato da tasiri a fannoni daban-daban bisa ga aikinsu gaba daya da tasirin su a shekara guda.
Jaridar Hukumar Jami’ar ta kara da cewa, wannan karramawa ta kara daga matsayin BUK a duniya, tare da tabbatar da matsayinta a matsayin cibiyar bincike da ilimi a Najeriya da Afirka.
