Allah Ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a cikin shirin Dadin Kowa rasuwa.
Bayanin hakan na cikin wani saƙo da fitacciyar marubuciya, Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook a da kuma karin bayani da wakilinmu ya samo daga abokan aikinsa daren ranar Lahadi.
“Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, yanzu muke samun labarin rasuwar Malam Nata’ala, Allah Ya gafarta masa, Allah Ya sa jinya ta zama kaffara.” In ji Fauziyya a sakon da ta wallafa
Jarumin ya jima a kwance yana fama da rashin lafiya, inda ya sha fitowa a cikin wasu faifan bidiyo yana neman taimakon jama’a kan rashin lafiyar da yake fama da ita.
Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗauki nauyin yi wa marigayin magani, bayan da marigayin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shugaban ƙasar Nijar, ya taimaka masa da kuɗi kimanin Naira miliyan 27 domin ya ci gaba da neman magani, bayan ya nemi taimakon jama’ar gari.
