Gobara da ta tashi a Kwalejin Kimiyyar Alkur’ani da Nazarin Addinin Musulunci mallakin Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Rafin Albasa dake Jihar. Ta kuma janyo mummunar hasara ga gine-gine da kayan makarantar.
jaridar WikkiTimes ta rawaito cewa, gobarar ta kama gine-ginen bene na makarantar inda ta shafi ofisoshi da ajujuwan karatu da dakunan gwaje-gwaje da dakunan kwamfuta da ɗakunan karatu da kuma ɗakin malamai dake saman bene.
Gobarar ta kuma cinye kayayyakin mallakar malamai da ɗalibai kamar tufafi, katifu, bargo da sauran muhimman kaya. Har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba.
Sheikh Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, Darakta Janar na Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kai ziyara tare da manema labarai domin duba barnar, inda ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa rashin asarar rai.
Ya ƙara da cewa gobarar ta shafi littattafan addini da dama, ciki har da wadanda Sheikh Dahiru Bauchi da’ya’yansa da wasu malaman addini suka rubuta.
Rahotanni sun ce Jami’an kashe gobara sun shafe fiye da sa’o’i uku suna ƙoƙarin shawo kan gobarar kafin su samu nasara.
