Majalisar Wakilai ta bukaci Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da ya
gabatar da kudurin hukunci mai tsauri kan masu sarrafa da shigo da jabun magunguna.
Majalisar na son a sa daurin rai da rai ga wadanda aka kama da laifin, tare da yin garambawul ga dokokin da ake da su.
Dan Majalisa Kabiru Alhassan Rurum ya ce, rashin hukunci mai tsauri ne ke haddasa yawaitar jabun magunguna a kasar.
Ya kuma ce, daukar matakin zai hana masu aikata laifin ci gaba da aikinsu.
Bayan doguwar tattaunawa, majalisar ta amince da sabon kudirin dokar.
