Ƴan Majalisar Wakilai ta ƙasa sun tara kuɗin ne daga albashinsu a matsayin gudunmawa ga ƴan Najeriya.
Za kuma su gabatar wa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kuɗin da suka tara a matsayin gudunmawarsu don ragewa ‘yan ƙasa raɗaɗin tsadar rayuwa da ake fama da ita.
Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar Alhamis.
“Yawan da kuɗin da muka tara sun kai Naira miliyan 700. Za kuma mu mika su ga shugaban kasa a ranar 31 ga watan Disamban 2024”. Inji shi.
A watan Yuli ne ƴan majalisar suka yi alƙawarin sadaukar da rabin albashinsu domin taimakawa ƴan ƙasa sakamokon cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.
