
Majalisar dokokin kasar nan ta sanar da dakatar da dukkan ayyukan majalis domin girmama marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a birnin Landan na ƙasar Ingila.
A wata sanarwa da Sakataren Majalisar Tarayya, Kamoru Ogunlana, ya fitar ga manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana alhinin da shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai ke ciki dangane da rasuwar tsohon shugaban.
Sakataren ya ce Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai sun umurci dukkan ‘yan majalisar da su sauya tsarin aikace-aikacensu don su samu damar halartar jana’izar tsohon shugaban.
Majalisar ta kuma miƙa sakon ta’aziyya a madadin dukkan mambobinta da ma’aikata ga Gwamnatin Tarayya da al’ummar Nijeriya da Gwamnatin Jihar Katsina da iyalansa da dangi baki ɗaya.