Majalisar dokokin Jihar Kano Kano dau alkawarin gaggauta amincewa da kasafin kudin da Gwamna Abba Kabir Yusif ya gabatar mata.
Za kuma ta yi haka ne don ganin kasafin kudin ya fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara.
Shugaban Majalisar Jibril Isma’il Falgore ne ya fadi haka bayan da gwamnan ya gabatar wa da majalisar kasafin kudin shekarar 2026 a ranar Laraba.
Majalisar ta lashi takobin yin taza da tsifa da daukar kuma dukkan matakan da doka ta tanada, wajen gaggauta amincewa da kasafin kudin
Falgore ya kuma bukaci dukkanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati da su kasance cikin shiri domin zuwa majalisar dan su kare kasafin kudin da suka yiwa ma’aikatun su na shekara mai kamawa.
Gwamnan ya gabatar wa majalisar kasafin kudin shekarar ta badi wanda ya zarce fiye da naira tiriliyan 1 da biliyan dari uku, na farko a tarihin jihar.
