Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta kira taron gaggawa a wannan Lahadin domin tattauna ƙudirin Isra’ila na ƙwace iko da Zirin Gaza.
Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da shi a karshen mako, ya jawo suka daga ƙasashen duniya.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya kwatanta shirin da abin da zai ƙara dagula lamura a fadan da aka kwashe watanni 22 ana yi.
Kasashen Turai da ke cikin Kwamitin Sulhun da suka hada da Denmark da Faransa da Girka da Burtaniya da Slovenia ne suka kira wannan zaman gaggawan a birnin New York na Amurka.
DW ya ruwaito cewa, dukkan mambobin Kwamitin Sulhun banda Amurka sun goyi bayan wannan zaman na yau Lahadi wanda zai dubi abinda ya dace a yi a kan yunkurin na Isra’ila.
