Majalisar Dattawa ta amince da bukatar bashin dala biliyan 6 da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar domin gudanar da ayyukan more rayuwa, biyan basussuka da kuma gyaran tashoshin jiragen ruwa.
Amincewar ta biyo bayan nazarin wasiƙu biyu da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar.
A wasiƙa ta farko, Shugaba Tinubu ya nemi amincewa da bashin dala biliyan 5 daga bankin First Abu Dhabi Bank da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ya bayyana cewa idan aka karɓi bashin gaba ɗaya, zai ƙara yawan bashin Najeriya daga dala biliyan 110.3 zuwa dala biliyan 115.3.
Ya kuma bukaci a yi amincewar cikin gaggawa, yana mai cewa za a tabbatar da bashin da takardun kudi na Naira.
A wasiƙa ta biyu, Shugaban ya nemi amincewar bashin dala biliyan 1 domin gyaran tashoshin ruwa na Lagos Port Complex da Tin Can Island Port.
An bayyana cewa bankin Citibank London ne ke shirya bashin, tare da goyon bayan UK Export Finance.
A cewar Tinubu, kudaden za su taimaka wajen zamanantar tashoshin jiragen ruwa, inganta ayyukansu, ƙara tsaro da kuma daidaita su da ƙa’idojin duniya.
Ya ƙara da cewa gyaran zai magance matsalolin da suka dade suna addabar tashoshin tare da ƙarfafa tattalin arziki ta hanyar bunƙasa harkokin kasuwanci da sufuri.
Shugaban ya kuma bayyana cewa bashin zai ɗauki shekaru 14 kafin a biya, ciki har da wa’adin shekaru huɗu na fara amfani da shi, tare da ƙarin kuɗaɗen kaso 1.1 cikin ɗari na karuwa da kuma kaso 1.07 cikin ɗari na kuɗin inshora na UKEF.
Tun da farko, shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan basussuka na cikin gida da na waje, Sanata Aliyu Wamakko, ya ce kwamitin ya yi cikakken nazari kan bukatun kafin gabatar da rahotonsa ga majalisar domin amincewa.
