
Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da bincike kan ƙaruwar koke-koken ’yan kasa kan yawan cire musu kuɗaɗe ba tare da bayani ba daga asusun ajiyarsu da bankunan kasuwanci ke yi.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da wani ƙuduri da ɗan majalisa Tolani Shagaya daga jihar Kwara ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan abin da ya kira, cire kuɗaɗe ba tare da bayani ba, da kuma yawan kuɗaɗen da ake karɓa ba bisa ka’ida ba, duk da dokokin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kafa.
Yayin gabatar da ƙudurin a zaman majalisa ranar Talata, Shagaya ya duk da cewa ana sa ran bankuna su bayar da muhimman ayyukan kuɗi cikin farashi mai sauƙi, yawancin ’yan Najeriya na fuskantar cire kuɗaɗe da dama.
“Cire kudade kamar kuɗin saƙon SMS da kuɗin gyaran kati da kuɗin kula da asusu da kuɗin canja wuri tsakanin bankuna da harajin hatimin da kuma wasu cire-cire da ba a bayyana ba, da dama daga cikinsu ana maimaita su ko ba a bayyana su yadda ya kamata ba”, in ji dan Majalisar
Bayan amincewa da ƙudurin, Majalisar ta bukaci CBN da ya fitar da jerin kuɗaɗen da aka amince da su cikin sauƙi ta yadda kowa zai fahimta, tare da tabbatar da aiwatar da hukunci ga bankunan da suka karya doka.
’Yan majalisar sun kuma bukaci babban bankin ƙasa da ya kafa wata hanya mai sauƙi da inganci don karɓar koke-koke daga abokan ciniki da suka fuskanci cire kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba ko fiye da kima.