Jakadan Amurka na Musamman kan Harkokin Larabawa da Afirka, Mista Massad Boulos, ya ƙaryata iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya babu gaira babu dalili.
Jakadan ya faɗi hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Jumma’a.
Mista Boulos, Mashawarci ne ga Shugaban Amurka Donald Trump.
“Waɗanda suka san Najeriya sosai sun fahimci cewa ta’addanci ba shi da launi, addini, ko ƙabila.
“Kungiyoyin Boko Haram da ISIS sun kashe Musulmai sama da Kiristoci. Mutane daga kowane ɓangare na fama da wannan tashin hankali. Ba a iya (wasu daban kadai) ake kai wa hari ba. In ji shi.
Jakadan ya bayyana cewa rikicin da ake samu a Arewa ta Tsakiya a Najeriya, rikici ne tsakanin manoma da makiyaya, wani lokaci yana shafar Kiristoci, amma asalin rikicin yana da nasaba da harkar noma, ba addini ba.
Ya kara da cewa, “Najeriya ƙasa ce da ta ƙunshi ƙabilu da addinai da dama waɗanda suke zaune tare tsawon shekaru. Bai kamata a juya wannan matsala zuwa ta koma ta addini ba.”
Boulos, ya yaba wa gwamnatin Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarin da ta ke yi wajen inganta tsaro, inda ya ce sakamakon ƙoƙarin ya fara bayyana.
Ana hasashen cewa, maganar “kisan gillar Kiristoci” a Najeriya ta fara ne ƙara ne bayan jawabin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) da aka yi a Amurka.
A yayin taron, Shettima ya yi kira da a samar da zaman lafiya a Gaza da kuma goyon bayan tsarin ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Falasɗinu. Shine ake yiwa Najeriya bita da kulli.
Sai ga shi a ‘yan kwanakin nan wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka nemi gwamnatin kasar ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashe masu hatsari wadda ake zaluntar Kiristoci.