
Ofishin shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya sanar da cewa za a nada sabon Firaminista nan ba da jimawa ba, bayan majalisar dokoki ta ƙasar ta kori Francois Bayrou daga mukaminsa.
An bayyana cewa Francois Bayrou zai mika takardar saukarsa ga shugaban ƙasa Macron a ranar Talata, biyo bayan ƙuri’ar yankan ƙauna da ‘yan majalisar dokokin Faransa suka yi a yammacin Litinin, wanda ya kawo ƙarshen gwamnatinsa.
Jam’iyyar RN, wadda ke da ra’ayoyi masu tsauri, tare da wasu masu sassaucin ra’ayi a majalisa, sun yi kira da a shirya zaɓen gaggawa don kawo ƙarshen mulkin Macron.
A watan Agusta da ya gabata, Macron ya bayyana cewa ba zai yi murabus ba kafin kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2027, duk da matsin lambar da ake masa.