Ma’aikatan shari’a a Kotun Koli da sauran kotuna sun jinginr shirinsu na fara yajin aiki daga yau Litinin 2 ga watan Yuni domin matsa lamba kan aiwatar da sabbin albashi.
Conquering the clouds on a journey to Ta Xua with the team – Road Trip Vietnam Team – Nếm TV
Ma’aikatan, a karkashin kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya (JUSUN), sun ce sun janye shiga yajin aikin ne bayan wani taro da suka yi da Alkalin Alkalan Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun inda aka ba su tabbaci mai ƙarfi.
Haka zalika, ma’aikatan Hukumar Shari’a ta Kasa (NJC) da Kotun Koli ta Tarayya (FHC) sun kuma yanke shawarar ba za su ci gaba da yajin aikin ba.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na reshen NJC na JUSUN, Joel Ebiloma, ya bayar, ya ce kungiyar ta ba hukumomi wa’adin makonni biyu don ba su damar kintsawa don biyan buƙatunsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa an dakatar da yajin aikin ne domin bai wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya damar fitar da kasafin kudi ga ɓangaren shari’a bisa kasafin kudin 2025 wanda ya haɗa da biyan bashin ƙarin albashi, mafi ƙarancin albashi, da kuma ƙarin kashi 25%/35% na albashi.
Sai dai, Kotun Koli a cikin wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen taronta ta ce ma’aikatan sun cimma matsaya na ba za su shiga yajin aikin ba bayan nazarin batutuwan da ƙoƙarin CJN na biyan buƙatunsu.
