Ma’aikatan jinya da ungozoma sun bai wa gwamnatin Kano wa’adin kwanaki 15 kafin tsunduma yajin aiki

0
118

Kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta kasa reshen Kano ta bukaci ‘ya’yan ta da su kasance cikin shirin ko ta kwana domin tsunduma yajin aiki nan da kwanaki sha 15 masu zuwa, matukar gwamnatin Kano ba ta saurari kokensu ba.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sanya hannun sakataren ta na Kano, kwamared Ahamd Hamzat Sharada.

Da yake yiwa wakilinmu Kamal Umar Kurna karin bayani kan abinda sanarwar ta kunsa, shugaban kungiyar na kasa reshen jihar Kano, kwamared Ibrahim Mai Karfi ya ce, sun dauki matakin bai wa gwamnatin Kano wa’adin kwana 15 domin ta biya musu bukatunsu, bayan tattaunawa ta tswon lokaci da wakilan ta ba tare da cimma wata matsaya ba.

Mai Karfi ya ce daukar matakin tafiya yajin aikin ya zama dole sbaoda yadda gwamnati ta Kano ta yi biris da bukatunsu tare da nuna musu rashin kulawar da ta dace akan ayyukansu, musamman yadda lamura ke cigaba da tabarbarewa a asibitocin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!