
Matashin tare da gwamnan jihar Yobe yayin da lambar shaidar kafa tarihi na a duniya da aka ba shi
Matashin ya shiga kudin ne da daukar hoto 897 a awa 1 da hakan ta sa ya doke mai rike da wannan kambun na duniya
Saidu Abdulrahman shine ya kafa wannan tarihi yanzu a duniya na mafi daukar hotuna kai tsaye cikin sa’a ɗaya.
Hakan ya bayyana a shafin matashin na Facebook a inda matashin ya wallafa wannan sanarwa tare da hotunansa dauke da takardar shaidar na shiga kundin abubuwan ban mamaki na duniya.
Sa’idu Abdulrahman mai shekara 28, ya ɗauki hotunan ne masu daukar hankali a watan Satumban 2023, lamarin da ya ba shi damar doke wanda ya lashe kambun na bara da hotuna 500.
“Na yi yunƙuri da kuma samun nasarar kafa tarihin ne domin in wayar da kan jama’a game da daukar hoto a Nijeriya”. In ji shi
Da wannan ƙwazo ne Kundin abubuwan bajinta Duniya na Guinness World Records (GWR) ya karrama matashin da lambar yabo.
An baiwa matashin lambar yabon ne a garin Potiskum babban Jihar Yobe a wani taron da ya samun halartar jami’an gwamnatin jihar da ɗalibai da kuma masoyansa.