Babbar kotun jihar Kano ta dage sauraren karar da aka shigar kan shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutane bakwai, bisa zargin cin hanci da almundahanar kudade.
Kotun ta dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar 15 ga watan Afrilu shekarar da muke ciki.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, zarge-zarge takwas ne gwamnatin jihar Kano ta gabatar kan Ganduje, da matarsa Hafsat Umar.
Sauran wadanda ake kara sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, da kamfunnan Lamash properties Limited, da Safari Textiles Limited da kuma Lasage General Enterprises Limited.
Tuni dai kotun ta tsayar da ranar 15 ga Afrilun shekarar da muke ciki domin ci gaba da sauraran karar da ake yiwa tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da karin wasu mutum bakwai ciki har da matarsa Hafsat Abdullahi Ganduje.
