
Gwamnatin Kano ta ce hukumar KAROTA na da hurumin kamawa da cin tara da kuma Ladabtar da masu karya dokokin tuki domin tsaftace harkar sufuri da titunan jihar.
Kwamishinan Sufuri na Kano Ibrahim Ali Namadi Dala ne ya bayyana hakan lokacin da yake karin bayani kan banbancin dake tsakanin hukumar KAROTA da sabuwar hukumar gudanarwar dokokin ababen hawa da majalisar dokokin Kano ta yi.
A zaman Majalisar Dokokin Kano na ranar Talatar ne, majalisar ta yi dokar kafa hukumar gudanarwar ababan hawa ta jihar, wadda aka dorawa alhakin kamawa da cin tara da kuma ladabtar da masu karya kowace irin dokar tuki a Kano.
A ganawar da Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin Kano, Lawan Hussaini Dala ya yi da ‘yan jarida a Talatar ya ce, aikin Hukumar KAROTA kawai shine hana cunkoso a kan titunan Kano.
Sai dai rahotanni sun bayyana musanta hakan da Kwamishinan Sufuri na Kano Ibrahim Ali Namadi Dala ya yi, tare da cewa idan Gwamnan Kano ya sanyawa sabuwar dokar hukumar hannu, za su tabbatar da cewa ayyukanta ba su ci karo da na hukumar KAROTA ba.