Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar LP, Datti Baba-Ahmed ya ce lokaci ya yi da za a bai wa sabbin jini dama a siyasar Najeriya.
Cikin wani bidiyon hirarsa da gidan Talbijin na Channels, Datti ya ce tun lokacin da yake yi wa ƙasa hidima (NYSC) Atiku Abubakar ke faman tsayawa takarar shugabancin ƙasa.
A cewarsa haka aka zo shekarar 2018 suka shiga zaɓen fitar da gwani tare da shi, haka ma a 2023 suka sake tsayawa takara da shi lokacin shi Datti na a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Datti Baba Ahmad yace tabbas a zaben nan akwai buƙatar bai wa sabbin jini damar gwada tasu sa’ar”, kamar yadda ya bayyana.
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasar ya ce akwai matasa sabbin jini masu zummar kawo gyara a siyasar ƙasar, amma yadda aka sanya tsarin zama mai wahala da tsauri na yi musu tarnaƙi.
