
Gidauniyar Mata Musulmi ta Jihar Kano (GMM) ta rubuta takardar korafi zuwa ga Gwamnatin Jihar Kano kan abin da ta bayyana a matsayin batanci ga Manzon Allah (S.A.W) da wasu malamai ke yi.
A cikin wasikar da aka aikewa Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Farouk Ibrahim, kungiyar ta bayyana cewa lamarin ya haifar da bacin rai da damuwa a zukatan Musulmi.
Sakatariyar kungiyar, Fatima Ibrahim Ilyas Dorayi ta ce, idan malaman da ake zargi suka kare kansu, hakan zai sa a kawo karshen wannan matsala.
Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Kano da kwamitin Majalisar Shura da su tsawatarwa malamai da mabiya da ke yada irin wadannan kalamai a kafafen kafafen sada zumunta.
Haka kuma ta jaddada bukatar gwamnati ta dauki tsauraran matakai wajen hana irin wannan hali domin kaucewa rikice-rikicen da ka iya tasowa a cikin al’umma.