Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2025 take son fara amfani da dokar haraji ta 2024.
Dokar harajin dake jiran amincewar majalisun kasa, ta kunshi sauye-sauyen haraji guda hudu da zasu kawo sauyi kan yadda ake karba da tasarrufi da hajarin da gwamnati ke karba.
Shugaban kwamitin fadar Shugaban kasa kan samar da sauye sauyen dokar harajin Mista Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a Legas.
Kwamitin shi ne ke Jagorantar gyare gyare a cikin dokar harajin wacce tasha zazzafar suka daga bangarori daban daban musamman Arewa.
Sai dai kurar ta fara lafawa ne bayan kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a ranar Alhamis ta goyi bayan dokar.
Majalisar dattijai kuwa a ranar Juma’a 17 ga watan Janairun shekarar 2025 ta bayyana gamsuwarta kan yadda gwamnonin suka amince da dokar harajin.
Shima Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa gwamnonin bisa hadin kan da suka nuna wajen amincewa da dokar tare da bukatar majalisar dattawa ta gaggauta amincewa da ita.
A ranar 28 ga watan Janairun 2025 majalisar dattawa za ta ci gaba da zama bayan kammala hutun Kirsimati da sabuwar shekara.
Oyedele, wanda yayi magana a wani taron masu ruwa da tsaki a Lagos ,ya ce ana sa ran majalisar zata amince da wannan doka kafin watan Maris, yayin da za a ci gaba da shirye-shiryen fara aiwatar da ita cikin watan Yuli.
Yace Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yana son fara amfani da dokar akan lokaci shiyasa ya tsayar da watan na Yuli.