
Rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi ta sanar da mika wuyan ‘yan Boko Haram 210 da kuma ƴan uwansu, a wani babban ci gaba da ke nuna tasirin samamen da dakarun ke kaiwa maboyar ‘yan ta’adda.
A cewar kakakin rundunar, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, waɗanda suka mika wuya sun amsa cewa sun taka rawa a hare-hare da dama a yankunan Bakatolerom da Barkalam da Litri da kuma Kaiga Ngbouboun da ke kewaye da tafkin.
Rundunar ta kuma ce, an kwato makamai 10 masu nau’o’i daban-daban daga hannun waɗanda suka ajiye makaman nasu ta sakamakon mika wuyan.
Kwamandan Sector 2 na Operation Lake Chad Manjo Janar Moussa Haussa ya yabawa dakarun bisa jajircewarsu, yana mai jaddada cewa “ta’addanci ba shi da makoma a yankin.”
Ya tabbatar da cewa waɗanda suka mika wuya za su shiga shirin sauya musu akida ko deradicalisation na MNJTF, tare da samun kulawa da mutunci.