
Rikicin cikin gida ya sake barkewa tsakanin mai magana da yawun gwamnan jihar Kano da kuma dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Kukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado.
A Wani Saƙo da mai magana da Kakakin Gwamna Sanusi Bature D/Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce, Mutuncin Dan Majalisa Tijjani Abdulkadir Jobe, a wajensa shi ne ya yiwa mutane abin da ya kamata, tun da akwai hakkin su a hannun sa.
An jima ana zargin Sanusi Bature da zawarcin kujerar Jobe hakan ta sa dangantaka tsakaninsu ta yi tsami.
Sai ga shi a wannan karon Bature ya fito fili ya bayyana dalilin rashin gamsuwa da salon wakilcin na Jobe.
A wani faifen bidiyo da ɗan majalisar ta taba saki, ya koka tare da zargin Baturen da yi masa zakon ƙasa.