Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027.
Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba da fifiko kan hadin kai da karfafa jam’iyyar a fadin jihar.
Ya ce suna matukar farin ciki da shugabancin jam’iyyar a jihar, sannan ya bukace su da su yi aiki tukuru don ganin an samu hadin kai a cikin jam’iyyar”.
Ya kara da cewa, dole ne jam’iyyar ta yi aiki da “zuciya daya” idan har tana fatan lashe zaɓukan jihohi da na kasa a 2027.
