
Ɗan majalisar wakilai Abdulmumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso bai rufe yiwuwar komawa jam’iyyar APC ba gabanin zaɓen 2027.
Kofa ya bayyana haka ne a yayin da ake hira da shi a shirin ‘Politics Today’ na Gida na Talbijin na Channels TV a makon nan.
“Tafiyar Kwankwasiyya na da ƙarfin siyasa da ba za a iya yin watsi da Kwankwaso ba.Duk da kasancewar Kwankwaso ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, har yanzu ya bar kofar tattaunawa a buɗe da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC. Komai yana yiwuwa a siyasa, kuma Kwankwaso bai taɓa rufe kofa ba,” in ji Kofa.
Sai dai ya yi nuni da yiwuwar wasu jiga-jigai a APC na Kano su yi adawa da dawowar Kwankwaso jam’iyyar saboda muradunsu na siyasa.
Kofa ya kuma kara da cewa, a matsayinsa na ɗan Kwankwasiyya, bai ga wani dalili da zai hana Tinubu neman wa’adi na biyu ba idan lokacin tazarce ya zo.
Kofa, wanda jigo ne a jam’iyyar NNPP, ya kuma sha ganawa da Shugaba Tinubu wanda hakan ba zai rasa nasaba da zawarcin Kwankwaso zuwa APC ba, in ji masu kula da alamuran siyasa.