Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba zai koma jam’iyyar APC ba sai an fayyace masa matsayinsa a jam’iyyar kuma an dawo masa da takardun manufofin da suka rubuta kan yadda za a tafiyar da rayuwar talakawan Najeriya.
Kwankwaso ya jaddada cewa dole ne a fayyace masa matsayin magoya bayansa da kuma gwamnatin jihar Kano kafin yanke duk wata shawara kan siyasa.
Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a gidansa da ke Miller Road, Kano, yayin da yake karɓar shugabanni da magoya baya daga ƙananan hukumomin Rano da Dawakin Tofa, tare da wasu mambobin tafiyar Kwankwasiyya da suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso ya ce burinsa shi ne kare muradun al’umma, musamman talakawa, tare da tabbatar da cewa duk wata tafiya ta siyasa za ta amfanar da magoya baya da jama’ar jihar Kano gaba ɗaya.
Wannan furuci na Kwankwaso ya zo ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yiwuwar sauya sheƙar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa APC.
