Kungiyar Kwankwasiyya ta soki matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi tare da mayar da ita karkashin Ma’aikatar Ilimi, tana mai cewa matakin na da alaka da siyasa kuma ba zai amfani cigaban al’ummar jihar Kano ba.
A cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Dr. Habibu Sale Mohammed, ya fitar a ranar Litinin, ya ce hujjar gyaran tsarin gudanarwa da gwamnati ta bayar ba ta bayyana ainihin dalilin daukar matakin ba.
Ya ce: “Rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da sunan sake fasalin gudanarwa ya jawo damuwa kan abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci da kuma yadda take tafiyar da al’amuran mulki.”
Kungiyar ta kuma yi zargin cewa matakin na da nasaba da rikicin siyasa da ya dabaibaye mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda a baya yake kula da ma’aikatar.
A cewar sanarwar: “Ba za a iya watsi da ra’ayin mutane ba dake cewa an dauki wannan mataki ne domin hukunta mataimakin gwamnan saboda kin barin tafiyar Kwankwasiyya da kuma burin magoya bayan da suka kawo wannan gwamnati mulki.”
Kungiyar ta kara da cewa tun sama da shekara guda da ta wuce an fara raunana ma’aikatar ta hanyar bada wasu umarni na gudanarwa da suka sa wasu hukumomi da sassa da ya kamata su rika kai rahoto ga ma’aikatar suka dai na, kuma suka rika kai rahoto kai tsaye ga gwamna.
A cewarsa, rushe ma’aikatar gaba daya na kara tabbatar da fargabar da ake da ita cewa ana tafiyar da harkokin gwamnati bisa lissafin siyasa maimakon muradun jama’a.
Ya ce: “Idan har akwai damuwa kan wanda zai kula da ma’aikatar, gwamna zai iya sauya wanda ke jagorantar ta kawai. Rushe ma’aikata mai muhimmanci ba shi ne mafita ba.”
Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan cewa an dauki wannan mataki ne a lokacin da har yanzu wasu manyan mukaman kwamishinoni a gwamnatin jihar ba su da masu rike da su.
A cewar sanarwar: “Gwamnatin da ta bar wasu muhimman ma’aikatun ba tare da kwamishinoni ba sannan kuma ta rushe wata muhimmiyar ma’aikata, ba za ta iya cewa tana bai wa cigaba muhimmanci ba.”
Kungiyar ta jaddada cewa bangaren ilimi mai zurfi na da matukar muhimmanci wajen bunkasar jihar Kano, tana mai cewa duk wani gyara a bangaren ya kamata ya kasance bisa tsari da shawarwari masu kyau, ba wai saboda siyasa ba.
