Ƙungiyar Kwankwasiya ta sanar da nadin tsoffin kwamishinonin gwamnatin Kano a wasu manyan mukamai, a wani mataki da ta ce na da nufin ƙarfafa tsarin jagoranci, inganta daidaito ne.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi.
An bayyana nadin AVM Ibrahim Umaru mai ritaya a matsayin Babban Jami’in Tsaron kungiyar. Dakta Yusuf Kofar Mata a matsayin Sakataren Kungiyar na Jiha, an kuma nada Nasiru Sule Garo ya zama Sakatare na CRC na jihar Kano.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, an nada Sanusi Surajo a matsayin Daraktan Wayar da Kai, sai Honarabul Adamu Kibiya wanda ya zama Sakatare na Kano PROPA, yayin da Mustapha Rabi’u Musa aka naɗa shi a matsayin Sakataren Kwankwasiya.
Ƙungiyar Kwankwasiya ta ce, nade-naden na nuna ƙudirin ta na ƙarfafa tsari, inganta dabaru da kuma ci gaba da tafiyar da manufofi da muradunta yadda ya dace.
Ƙungiyar ta kuma taya sababbin shugabannin murna, tana mai bayyana tabbacin cewa za su aiwatar da ayyukan da aka ɗora musu cikin ƙwazo da gaskiya, domin cigaban ƙungiyar da magoya bayanta.
