Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin gudanar da wani zama na musamman domin tattauna halin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar Sudan.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Sudan ce ta nemi a kira zaman, a daidai lokacin da rikici tsakanin sojojin ƙasar da ’yan tawayen RSF ke ci gaba da kai munanan hare-hare ga sojoji da farar hula da ya daidaita kasar.
A cewar majiyoyi, bangarorin biyu na ci gaba da fafatawa domin karɓe iko da muhimman yankuna a sassa daban-daban na Sudan.
Ana kai hare-hare da manyan makamai ciki har da atilare, roka, da jirage marasa matuka, inda fararen hula ke fuskantar mafi munin tasiri sakamakon rikicin.
Kwamitin Tsaron zai saurari bayani daga wakilan gwamnatin sojoji ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulfatta al-Burhan, da kuma na bangaren RSF karkashin Muhammad Hamdan Dagalo, domin tattauna hanyoyin rage tashin hankali da kuma tabbatar da samun damar kai kayan agajin jin kai, musamman abinci da magunguna, ga al’ummar Sudan.
