
Tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce sama da kungiyoyin ta’addanci 1,000 ne ke ci gaba da tayar da hankulan al’umma a nahiyar Afrika.
Ya bayyana haka ne ranar Litinin a taron hafsoshin tsaro na Afrika da ke gudanar a Abuja.
Gambari ya bukaci shugabannin kasashen Afrika, su fara tsare kasashensu kafin batun tsaron yankin gaba daya.
Ya jaddada bukatar samar da masana’antu da fasahohin tsaro na cikin gida domin yaki da ta’addanci.
A nasa bangaren, babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce matsalar tsaro a Afrika ba ta da iyaka, don haka hadin kan kasashe ya zama wajibi.
Taron na samun halartar wakilai daga kasashen Afrika 36, sai dai Mali da Burkina Faso ba su halarta ba.