Haɗakar ƙungiyoyin ma’aikatan ɓangaren lafiya ta bayyana cewa za ta ci gaba da yajin aikin da ta fara, bayan tattaunawar da ta yi da gwamnatin tarayya ta kare ba tare da cimma wata matsaya ba.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na kasa ya sanya wa hannu, wadda aka aikawa shugabannin kungiyoyin lafiya a fadin tarayyar kasar.
Sanarwar ta ce ƙungiyar ta gudanar da taro na tsawon sa’o’i uku a jiya Laraba, amma duk da tattaunawar, ba a samu daidaito kan batun hakkokin ma’aikata ba.
Sakataren ya bayyana cewa shugaban haɗakar ƙungiyoyin, Kwamred Kabiru Ado Minjibir, shi ne ya bayar da umarnin ci gaba da yajin aikin har sai an biya bukatun mambobin ƙungiyar.
Hadakar kungiyoyin bangaren ma’aikatan lafiya sun fara yajin aikin ne tun ranar Asabar, 15 ga Nuwamba, bisa ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da gyare-gyaren da suka shafi tsarin biyan albashi na tsawon shekaru goma sha biyu.
