Fiye da ƙungiyoyi 130 na jinƙai na fararen hula sun bukaci a gaggauta dakatar da aikin Gaza Humanitarian Foundation (GHF), wani shiri na agaji da Isra’ila da Amurka ke marawa baya, suna mai cewa tsarin yana barazana ga rayukan fararen hula a Gaza.
A cewar rahotanni ƙungiyoyin da suka haɗa da Oxfam da Save The Children da kuma Amnesty International, fiye da Falasdinawa 500 ne suka mutu tun bayan fara aikin GHF a ƙarshen watan Mayu. Haka kuma, sama da mutane 4,000 sun jikkata yayin da suke ƙoƙarin karɓar agaji a wuraren rabon kayan tallafi na kungiyar.
Ƙungiyoyin sun zargi dakarun Isra’ila da wasu ’yan bindiga da buɗe wuta a kan mutanen da ke jiran agaji, musamman a yankunan da aka ware domin rabon kayan abinci.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa an harbi mutane a lokacin da suke kokarin shiga ko fita daga wuraren rabon abincin agajin.
Isra’ila ta musanta zargin cewa sojojinta na harbin masu karɓar agaji da gangan, tana mai cewa tsarin GHF yana bai wa jama’a taimako kai tsaye ba tare da tsoma bakin Hamas ba.
