
Kungiyar tuntuɓa ta Arewa ACF ta yi kira kan yadda za a faɗakar da mutanen Arewa game da muhimmancin kare kansu, ganin yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a yankin.
Da yake jawabi a taron kwamitin zartarwa na ƙungiyar, shugaban ACF, Mamman Osuman SAN, ya koka kan yadda hare-hare, satar mutane da kisan-gilla suka zama ruwan dare a yankin.
Ya buƙaci shugabanni, masu ruwa da tsaki da al’umma su haɗa kai wajen magance matsalolin.
Ya ce dole ne su ilimantar da mutane kan muhimmancin kare kansu kuma mu samar da dabaru don yaƙar waɗannan matsaloli da Arewa ke fama da su da suka hada da barazanar yan bindiga, yan ta’adda da masu satar mutane.
Mamman Osuman, ya yi gargaɗin cewa matsalar tsaro ba ta tsaya a iya Arewa kawai ba, matsala ce ta ƙasa baki ɗaya da ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa saboda haka ya ce dole ne gwamnoni, yan majalisa da sarakunan gargajiya su yi aiki tare don magance waɗannan matsaloli.
Sai dai ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan ɗaukar matakan gaggawa maimakon jiran mafita ta siyasa.