Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar mata dake inganta koyo da koyarwa tsakanin malamai da dalibai (KALAMED) ta horas da mata fiye da 20 dinka kunzugun al’ada.
An gudanar da horaswar ne ga mambobin kungiyar Dorayi Bedsheets Makers Association dake unguwar dorayi ranar Alhamis.
Da take jawabi shugabar kungiyar Hannatu Sulaiman Abba ta ce sun koyar da matan yadda zasu rinka dinka kunzugun al’ada wanda za a iya wankewa duba da cewa da yawan mata basa iya sayen wacce ake amfani da ita sau daya saboda tsadar ta.
Ta ce Kalamed ta shirya taron ne a cigaba da bikin ranar mata ta duniya tare da hadin gwiwar kungiyar G100.
Hannatu Sulaiman Abba wacce ke cikin masu wayar da kai dangane da hanyoyin kula da kai yayin jinin al’ada a kungiyar PSI Nigeria ta kara da cewa ta ji dadin yadda matan suka yi saurin koyan.
Daya daga cikin wadanda aka koyar Sahura Abdullahi Zakariya, ta ce zasu yi amfani da abinda suka koya wajen samar da kunzugun al’ada na mata domin tallafawa mata marasa karfi.
Ta ce suma zasu yi kokarin koyar da wasu yadda ake hadawa.
A nata bangaren shugabar kungiyar Dorayi Bedsheets Makers Association Kwamaret Aisha Muhd Mustapha, ta ce akwai takaici yadda wasu matan basa iya sayen auduga lokacin al’ada saboda tsadar ta.
Ta ce irin wannan kunzugu da aka koya musu yana da sauki kuma zai rage wahalar da mata suke sha wajen saye.
Ta kuma ci yin hadin gwiwa musamman da masu ruwa da tsaki da kungiyoyi domin koyar da dalibai mata dake makarantu yadda zasu rinka hadawa da kansu.
