
Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar kwallon kafa ta tubabbun ‘yan daba ta Tudun Muntsira da gwamnatin Kano ta yiwa afuwa, ta lallasa jami’an tsaro a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Kungiyar ta yi nasara a wasan da Ma’aikatar Yada Labarai Da Al’amuran Cikin Gida ta jihar Kano ta shirya a yammacin ranar Litinin, a wani bangare na murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya da ake yi a ranar 1 ga watan Oktoba.
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Tudun Muntsira (Safe Carridor) Auwalu Rabiu Uwar Zuma, a jawabinsa, ya bayyana farin cikinsu bisa yadda gwamnati ke samar da shirye-shiryen sauya musu dabi’u zuwa na gari.
”Sakamakon shirin gwamnatin Kano na Tudun Muntsira suka ajiye makamansu tare da rungumar zaman lafiya”. In ji shi.
Yayin da Kwamishinan Yada Labarai Da Al’amuran Cikin Gida kwamaret Ibrahim Abdullahi Waiya, a jawabinsa jim kadan bayan tashi daga wasan, ya ce sun shirya wasan ne don janyo matasan kusa da jami’an tsaro tare da kara samun fahimtar juna.
”Gwamnati na da yakinin matasan na da rawar da za su taka wajen cigaban Jihar Kano. Ba daidai bane a kyale matasan na yin abin da bai dace ba wanda hakan ya sa muka fito da shirin Tudun Muntsira”. In ji kwamishina Wayya.
Ya kuma ce, ana samun nasarar shirin domin kuwa matasa na kawo kansu tare da ajiye makamansu.
Kwamishinan ya kuma baiwa matasan kyautar kofi da naira dubu 250, yayin da aka baiwa ‘yan wasan jami’an tsaro naira dubu 150.