
Ƙungiyar Inuwar lauyoyin Kano ta mika bukatar sake cigaba da bincike kan zarge zargen da aka yiwa dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada Alhassan Ado Doguwa tare da sauran wadanda ake zargi.
Cikin takardar korafin da kungiyar ta mikawa ofishin kwamshinan shari’a na Jiha kuma babban lauyan gwamnati, mai kwanan watan 11 ga watan satumba, kungiyar ta ce mutane da dama sun rasa ransu a zaben 2023 a Kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa, kuma wadanda suka shaida yadda abun ya faru da iyalan mamatan sun zargi dan majalisa mai waklitar yankin a majalisar tarayya Alhassan Ado Doguwa tare da wasu mutane da hannu a lamarin.
Sai dai sun yi zargin duk da girman tuhumar da ake musu, daga bisani an yi watsi da shari’ar saboda dalilai na siyasa, wanda hakan ya saba da sashi na 33(1) na kundin tsarin mulkin kasa da ya baiwa kowa damar rayuwa.
Takardar koken da daya daga cikin shugabannin kungiyar Dr Jafar Sadiq ya sanyawa hannu, ta roki kwamshinan shari’an Kano da ya sake bude tare da cigaba da wannan shari’a ta zargin kisan mutane yayin zaben 2023 a Tudun Wada da Doguwa.
Sannan a baiwa jami’an tsaro cikakkiyar damar gabatar da bincike ba tare da katsalandan ba.
Da kuma gurfanar da Alasan Ado Doguwa da dukkanin wadanda ake zargi gaban kotu muddin aka same su da laifi. Domin tabbatar da adalci ga iayalan wadanda aka kashe.
