
Hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano (SUBEB) ta hankalin kungiyoyin al’umma da ke kokarin mayar da wasu kananan makarantun sakandare da ke karkashin hukumar zuwa manyan makarantun sakandare, ba tare da la’akari da tanadin dokar Ilimi ta kasa ba.
Shugaban hukumar Yusuf Kabir, ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kai na hukumar Balarabe Danlami Jazuli ya fitar.
Yusuf Kabir, ya ce wannan yinkuri ka iya maida hannun agogo baya wajen cigaban ilimi.
Ya ce dokar ilimi ta kasa itace ta yi tanadin cewa makarantun firamare da kananan makarantun sakandire suna karkashin hukumar ilimin bai daya a dukkanin jihohi bisa kulawar sassan ilimi na kananan hukumomi (LEA).
Ya ce su ma manyan makarantun sakandire dokar ta hannanta su ga wata hukumar ta daban da ke kula da su.
Ya ce wannan yinkuri na ganin an daga likafar kananan makarantun sakandire zai janyo koma baya ne kawai ga bangaren ilimi.
Ya ce hukumar ilimin bai daya zata cigaba da hada kai da hukumar ilimin bai daya ta kasa wajen ciyar da ilimi gaba.
Ya ce ba zasu taba lamuntar janye ikon kula da kananan makarantun daga hannun hukumar SUBEB ba.
Malam Yusuf Kabir ya kuma yi kira ga kungiyoyin da ke da niyyar kafa manyan makarantun sakandare a yankunansu da su fara tunanin yadda za su samar da dakunan karatu (ajuwuwa) a wani wurin na daban, domin hakan zai bayar da damar bude musu manyan makarantun sakandare ta hannun Hukumar da ke lura da irin wadannan makarantu a matakin jiha.