
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na tafiyar da harkokin gwamnati a bayyane sakamakon daukar shugabanci bisa gaskiya da amana.
Gwamnan ya bayyana haka yayin taron karawa juna sa ni na kwanaki biyu da ma’aikatar yada labarai karkashin jagorancin kwamishina Ibrahim Abdullahi Waiya ta shiryawa kungiyoyin fararen hula 250.
Taron wanda ake gudanarwa a jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu ya samu halartar kungiyoyin fararen hula daga jihohi daban daban na kasar nan.
Taken taron shine Karfafa kungiyoyin farar hula a Kano domin samar da ci gaba da habaka hadin kai wajen karfafa shiga dimokuraɗiyya da cigaba tun daga tushe.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce gwamnati na ganin kungiyoyin fararen hula a matsayin abokan hulɗa wajen tabbatar da ci gaban jihar, tare da bin diddigin duk wani mataki da gwamnati ke dauka domin ganin an samu gaskiya da adalci a tafiyar da mulki.
Mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin Kano ta ‘yan gwagwarmaya ce, yana mai cewa kowa a gwamnatin gwagwarmaya ya keyi domin kawo cigaba mai dorewa.
Kwamared Gwarzo yace irin wannan gwagwarmaya na kwatowa takala ‘yan cinsa shine ke tabbatar da dorewar demokaradiyya, musamman bangaren ilimin talaka da lafiyarsa da sauran bukatu.
Ya bukaci kungiyoyin su kauda kwadayi da son kai yayin da suke aiyukan sun a gwagwarmaya don samun cigaba.
A nasa bangaren kwamishinan ya da labarai na Kano Ibrahim Abdullahi Wayya ya ce taron zai ƙarfafa fahimtar juna tsakanin gwamnati da al’umma, musamman ta fuskar isar da sahihan bayanai da kuma ƙarfafa dimokuradiyya.
Waiya yace duk wata gwamnati da ta hada kai da kungiyoyin fararen hula to wannan gwamnatin bata shayin fito da abinda ta keyi a fili kowa ya gani.
Ya ce gwamnatin Kano ta fito da tsare tsare da suka sha bambam da sauran jihohi a Najeriya musamman tsarin bayar da kwangila ta yadda ake gudanar da komai a bayyane.
Yayin taron masana sun gabatar da makaloli daban daban kan yadda za a bunkasa aiyukan kungiyoyin farar hula da samar da cigaba.



