Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin kwace kadarori guda 57 mallakin tsohon Ministan Shari’a na Tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, SAN, tare da ’ya’yansa biyu, a matakin wucin-gadi.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa akwai zargin an mallaki kadarorin ta hanyoyin da ba su dace ba.
Hukuncin ya biyo bayan bukatar da lauyan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Barista Ekele, ya gabatar a gaban kotun.
A wata sanarwa da EFCC ta fitar, hukumar ta bayyana cewa an kiyasta darajar kadarorin da aka bayar da umarnin kwacewa ta haura naira miliyan dari biyu.
Kadarorin dai suna warwatse a jihohin Kebbi, Kano, Kaduna, da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Hukumar EFCC ta kara da cewa kwace kadarorin na wucin-gadi ne, yayin da ake ci gaba da shari’ar domin tantance sahihancin mallakarsu da kuma binciken zargin almundahana.
Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga Janairu, domin ci gaba da shari’ar da kuma jin karin bayani daga bangarorin da abin ya shafa.
