Kotun Koli ta kori karar tsige Shugaba Tinubu
Kotun koli ta kori da aka kai gabanta ana neman tsige shugaban kasa Bola Tinubu.
Wani ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019 ƙarƙashin jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP), Cif Ambrose Albert Owuru ne ya shigar da karar Inda yake neman kotun da ta tsige Tinubu bisa wasu manyan dalilai guda biyu.
Mai karar yana zargin shugaba Tinubu da rashin cancantar rike ofis din Shugaban kasa da kuma dare kujerar mulki ba tare da bin ka’ida ba yadda ya kamata
Mai karar na roƙon Kotun da ta soke cancantar Tinubu saboda batun kwace Dala $460,000 a Amurka da shugaban yayi a bisa zargin laifin safarar miyagun ƙwayoyi.
Da kuma zargin zama dan leken asirin Hukumar Leken Asiri ta CIA a Amurka
Sauran wadanda ake karar sun haɗa da tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Babban Mai Gabatar da Kara na Tarayya kuma Ministan Shari’a da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Sai dai a zamanta na dau litinin kotun ta kori karar, inda ta bayyana cewa masu kara sun gaza kawo hujjojin da suka gamsar da kotun.