Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa Abdulmalik Tanko, wanda aka samu da laifin yin garkuwa da kuma kashe yarinya ‘yar shekara takwas, Hanifa Abdussalam.
Mai shari’a A.R. Muhammad ne ya bayyana hakan yayin yanke hukuncin, inda ya ce kotun ta gamsu da shaidun da aka gabatar a shari’ar, tare da tabbatar da cewa hukuncin da Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke ya dace da doka.
Kotun ta tabbatar da laifukan da aka tuhumi Abdulmalik Tanko da su, waɗanda suka haɗa da garkuwa da kuma kashe marigayiya Hanifa Abdussalam, lamarin da ya girgiza al’umma a lokacin da ya faru.
A yayin yanke hukuncin, Mai shari’a A.R. Muhammad ya ja hankalin gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakin aiwatar da hukuncin kisa kamar yadda doka ta tanada, domin tabbatar da adalci, da kuma kare rayuka da tsaron al’umma.
