Babbar kotun tarayya a Kano karkashin Mai shari’a Adam Abdullahi ta yankewa wasu mutane hudu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari tare da tarar naira 10,000 kowannensu, bayan samun su da laifin fashi da makami.
Mutanen da aka yankewa hukuncin sun hada da Shafi’u Abubakar, Usman Suleiman, Usman Sa’idu da Ali Isa, wadanda mazauna unguwar Rijiyar Lemo ne a Kano.
An gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki domin aikata laifi da kuma fashi da makami, laifukan da suka saba doka karkashin sashe na 97 da 298(c) na kundin Penal Code.
A ranar 22 ga watan Yuli 2024, tsakanin karfe 3:00 zuwa 4:00 na dare, masu laifin sun shiga wasu gidaje dauke da muggan makamai a unguwannin Bankaura da Sabon Garin Doka da ke karamar hukumar Ungogo.
A cewar takardar tuhumar farko, masu laifin sun kai hari gidajen,Malam Abdullahi Musa da Mansur Mu’azu, tare da kwace musu kayayyaki masu daraja.
A tuhuma ta biyu, kotu ta tabbatar da cewa sun sace wayoyi guda biyu, babur kirar Lifan mai darajar naira 700,000 da kuma kudi daga hannun Abdullahi Musa.
Sai kuma a tuhuma ta uku, an ce sun kwace kudin naira 201,000 da kuma kudin CFA 500 daga hannun Mansur Mu’azu a gidansa da ke Sabon Garin Doka.
Lauyan gwamnati, Barrista Ibrahim Garba Arif, ya gabatar da shaidu guda biyu domin tabbatar da zargin.
Sai dai lauyan wadanda ake kara, Barrista Basira Yunus, ta bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun sauya matsayinsu inda suka amince da zargin da ake musu.
Bayan nazarin shari’ar, kotun ta same su da laifi a dukkan tuhume-tuhumen, tare da yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari da kuma biyan tarar naira 10,000 kowannensu kan kowane laifi.
Kotun ta kuma umarci cewa za a gudanar da hukuncin ne a lokaci guda (concurrently), daga ranar da aka kama su, wato 22 ga watan Yuli 2024.
