
Babbar Kotun Jihar Katsina ta yanke hukuncin kisa ga mutum biyu da aka samu da laifin kashe tsohon kwamishinan kimiyya da fasaha, Injiniya Rabe Nasir, wanda aka kashe a shekarar 2021.
Mai shari’a Ibrahim Mashi na kotu mai lamba 9 ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa Shamsu Lawal da Tasi’u Rabi’u sun aikata kisan ne cikin shiri da nufin hallaka.
Shamsu Lawal, wanda shi ne tsohon mai gadi a gidan marigayin, da Tasi’u Rabi’u, wanda ke aiki a matsayin mai dafa abinci, sun amsa cewa sun aikata laifin ne bayan yunkurin sata daga gidan ya ci tura.
Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa bayan ƙin samun damar sace dukiya, sai suka shirya hallaka Rabe Nasir ta hanyar sa masa guba a cikin abincinsa.
Binciken hadin gwiwa tsakanin rundunar ‘yan sanda da asibiti ya tabbatar da cewa an samu sinadarin guba a jikin mamacin.
Kotun ta bayyana cewa kisan ya kasance da gangan, kuma an shirya shi da haɗin kai, wanda hakan ya sa aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Baya ga haka, kotun ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari kan wani tsohon mai gadi, Sani Sa’adu, bayan an same shi da laifin boye gaskiyar kisan da kuma hana gudanar da bincike cikin gaskiya.
Lauyan masu laifi, Ahmad Murtala Kankia, ya roƙi kotu da ta sassauta hukuncin, yana mai cewa wadanda ake tuhuma suna da iyali da masu dogaro da su.
Injiniya Rabe Nasir ya rike mukamin kwamishinan kimiyya da fasaha a lokacin mulkin tsohon Gwamna Aminu Bello Masari, kafin rasuwarsa.