Wata Babbar kotun tarayya ta rushe zaben cikin gida na shugabancin jam’iyar PDP da aka gudanar a jihar a bisa korafin rashin sahihanci.
Babbar Kotun wacce ke zamanta a Abakaliki babban birnin jihar ta rushe zaben ne a ranar Litinin tare da umartar hukumar INEC da kar ta karbi wadanda aka zaba a matsayin shugabanni.
Hakan ya biyo bayan ƙarar da wani mai suna Nnenna Lynda da wasu mutane 12 suka shigar suna ƙalubalantar sahihancin zaɓen.
Mai shari’a Hilary Oshomah ya haramta wa sabbin shugabannin jam’iyyar da aka zaɓa a jihar bayyana kansu a matsayin ‘yan kwamitin gudanarwa na jihar.
Lauyan masu ƙarar sun nemi kotu da ta yi watsi da zaben a bisa dalilin cewa an hana waɗanda yake kare wa sayen fom din takarar shugabancin jam’iyar. Duk da cewa ƙorafin da suka shigar yana gaban kotu jam’iyar ta yi kanta ta gudanar da zaɓen.