Babbar kotun tarayya ta haramta wa hukumar kula da lafiyar ababen hawa VIO tsayarwa ko kamen ababen hawa a kan hanyoyi.
Mai shari’a Evelyn Maha ta kotun da ke Abuja ta kuma haramta wa hukumar sanya tara a kan masu ababen hawa.
Alƙalin ta sanar da haka ne a yayin da take yanke hukunci kan ƙarar da wani mai fafutikar kare haƙƙin ɗan Adam, Abubakar Marshal, ya shigar kan hukumar VIO.
Kotun ta bayyana cewa babu dokar da ta bai wa hukumar ko jami’anta su tsayar ko su kama ababen hawa a kan hanya ko su tara.