Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranar 15 da 16 ga Nuwamba a Ibadan, jihar Oyo.
A hukuncin da aka yanke a ranar Juma’a, Mai shari’a James Omotosho ya bayyana cewa jam’iyyar ta karya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, da ka’idojin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da kuma kundin tsarin mulkinta, saboda ta kasa gudanar da sahihin zaɓe a jihohi kafin shirya babban taron kasa.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito Alkalin na cewa, ci gaba da shirya babban taron ba tare da gyara wadannan kura-kurai ba zai zama keta ka’idar bin doka da kuma dimokuradiyya a cikin jam’iyyar.
