Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ta amincewa jam’iyyar da ta gudanar da babban taronta na ƙasa kamar yadda tsara.
Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A. L. Akintola, a hukuncin da kotun ta yanke,
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook, ta kuma ce kotun ta umarci jami’an jam’iyyar da wakilanta da su guji duk wani yunƙuri na daƙile ko rusa jadawalin da aka tsara tun farko dangane da taron,
Ta kuma bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) umarnin tura jami’anta domin sa ido da lura da duk abin da zai gudana a yayin taron, domin tabbatar an kiyaye doka da ka’ida.
Mai Shari’a Akintola ya ce hakan zai taimaka wajen “inganta gaskiya da bayyana ainihin abin da ke faruwa a lokacin taron.”
Haka kuma, kotun ta umarci Umaru Ahmadu Fintiri, wanda ke shugabantar kwamitin shirya taron, da ya ci gaba da shirye-shiryen da suka shafi gudanar da babban taron, ba tare da tangarda ba.
Jam’iyyar ta tsara gudanar ta babban taron ne a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025, a filin wasa na Lekan Salami, Adamasingba.
Wannan hukuncin ya kawo ƙarshen duk wasu matsalolin doka da ke neman jinkirta taron ko kuma hana shi gaba daya.
Aminiya ta rawaito jam’iyyar na cewa, hukuncin kotun babbar nasara ce gare ta, domin yanzu kwamitin shirya taron (NCOC) na da damar kammala shirye-shiryen karɓar wakilai sama da 3,000 da ake sa ran halartarsu daga jihohi daban-daban.
