Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba hukumar EFCC umarnin cigaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Bayan shafe watanni yana boye tsohon gwamnan ya shiga hannun hukumar a ranar Talata, ta kuma gabatar da shi gaban alkali a ranar Larabar makon nan.
Mai shari’a Maryanne Aninih, ta umarci EFCC da ta cigaba da tsare tsohon gwamnan
Lauyoyin EFCC da na Bello sun yi muhawara kan buƙatar bayar da belinsa. A inda Lauyan Bello, Joseph Daudu (SAN), ya roƙi kotun ta bayar da belinsa kasancewar laifukan da ake tuhumarsa na cikin waɗanda za a bayar da beli.
Sai dai lauya mai gabatar da ƙara, Kemi Pinheiro (SAN), ya ƙalubalanci buƙatar hakan.
Daga baya kotun ta sa ranar 10 ga watan Disamba domin yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin.
Bello, tare da wasu tsoffin jami’an gwamnatin Kogi, Abdulsalami Hudu da Umar Oricha, an zarge su da haɗa kai wajen amfani da kuɗaɗen gwamnati don sayen kadarori a Abuja da Dubai, na kimanin Naira biliyan 110.4.
Kafin fara zaman kotun, an tsaurara tsaro a wajen kotun, inda jami’an sojoji, DSS, EFCC, da ‘yan sanda suka yi dafifi.