Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ayyana dan majalisar dokokin Jihar Filato dake wakiltar mazabar Jos ta Arewa, Adamu Aliyu, a matsayin wanda take nema a ruwa jallo, bisa zargin hannu a wata badakalar kwangilar TETFund ta sama da Naira miliyan 73
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin, bayan hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta shigar da bukatar hakan.
Takardun kotu da ta gani, wani ɗan kasuwa mai suna Mohammed Jidda ne ya kai korafi ga ICPC yana zargin cewa dan majalisar ya yi masa alkawarin taimakawa wajen samun kwangilar Naira miliyan 850 a TETFund
A binciken da ICPC ta gudanar, ta gano cewa Naira miliyan 47.8 an biya su cikin asusun dan majalisar, wani Naira miliyan 22.4 an biya shi cikin asusun wani kamfani
Hukumar ICPC dai tace tana da sahihan bayanan sirri cewa dan majalisar ya shirya tserewa ƙasar. Saboda haka ta roƙi kotu ta ayyana shi ana nemansa.
