Daga Fatima Hassan Gagara
An shirya fara zagayen fidda da gwani na gasar Kofin Duniya na mata ‘Yan kasa da shekaru 17 ta FIFA 2025 a ƙasar Maroko.
A wannan zagayen, ‘yan wasan Najeriya, Flamingos, da na Italiya a cikin ɗaya daga cikin fitattun wasannin zagaye na 16 na fidda gwani.
An tsara buga wasan ne a ranar Talata, 28 ga Oktoba, a filin wasa na Stade Olympique dake birnin Rabat, da ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya.
Najeriya ta samu damar shiga wannan zagaye bayan nasara mai ban sha’awa da suka yi da ci 4–0 kan Samoa a Rabat ranar Asabar.
Flamingos za su yi ƙoƙari su ci gaba da gina kan kyakkyawan sakamakon da suka samu a zagayen rukuni yayin da suke neman lashe kofin duniya na farko a tarihin ƙasar.
Ƙasar Maroko, wacce ita ce mai masaukin baki, za ta buga nata wasan a wannan daren, inda za ta kece raini da Koriya ta Kudu a filin Mohammed VI Football Academy Pitch 2 da ke Sale. Ana sa ran masoyan gida za su cika wajen domin goyon bayan Atlas Lionesses.
A farkon ranar Talata, Brazil za ta fafata da China PR, yayin da Amurka za ta kara da Netherlands, duka wasannin za a buga su da ƙarfe 4:30 na yamma a Sale.
A ranar Laraba, 29 ga Oktoba, Mexico za ta kece raini da Paraguay da ƙarfe 4:30 na yamma, yayin da Spain, wacce ke rike da kofin yanzu, za ta buga da Faransa a karawar ƙasashen Turai mai matuƙar jan hankali.
Daga baya a daren, Canada za ta kara da Zambia, sannan Japan, ɗaya daga cikin manyan ‘yan takarar gasar, za ta fafata da Colombia domin kammala zagayen na 16.
Dukkan wasannin za a buga su ne a filayen dake garin Rabat da kuma Sale, kuma ana iya kallonsu kai tsaye ta manyan tashoshin wasanni na duniya da kuma dandalin FIFA na intanet.
Yayin da gasar ke shiga muhimmin mataki, nasara hudu kawai ke tsakanin ƙasashe 16 da saura da lashe kofin Kofin Duniya ta Mata ‘Yan kasa da Shekaru 17.
Ƙasashe takwas masu nasara a zagayen 16 za su shiga zagayen ƙarshe na takwas (quarter-final) wanda zai fara ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025.
