An shiga rana ta biyar da gwamnatin ƙasar Iran ke ci gaba da katse intanet a faɗin ƙasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da ake cewa ita ce mafi girma a Iran cikin sama da shekaru uku.
Ƙungiyar sa ido kan harkokin intanet ta NetBlocks ta tabbatar da cewa har zuwa jiya Litinin, katsewar intanet ɗin na ci gaba da kasancewa a sassa da dama na ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa matakin na zuwa ne yayin da dubban ’yan ƙasar Iran ke ci gaba da fitowa kan tituna domin nuna adawa da manufofin gwamnati, duk da ƙoƙarin hukumomi na takaita sadarwa da yada labarai.
Masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun bayyana damuwa cewa katse intanet ɗin na iya ƙara ta’azzara take haƙƙin bil’adama, tare da hana duniya samun cikakken bayani kan halin da ake ciki a Iran a halin yanzu.
